Labarai
‘Yan jarida sun cancanci ingantacciyar rayuwa- Minista
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/10/IMG_20231019_165450.jpg)
Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta ce ‘yan jarida kasar na aiki cikin mawuyacin yanayi, in da a yawancin lokuta sukan rasa rayukan su yayin gudanar da aikin nasu.
Ministan Yaɗa Labarai da wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Idris ya ce sun can-canci samun ingantacciyar rayuwa, yadda za su samu damar gudanar da ayyukan su cikin sauƙi da walwala, a kan haka ne ya ce zai yi iyakar ƙoƙarin sa domin inganta rayuwar ‘yan jarida a gwamnatance.
Rahoton: Sunusi Shuai’abu Musa
You must be logged in to post a comment Login