Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan jarida sun yiwa kalamaina gurguwar fahimta – Tinubu

Published

on

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Tinubu, ya ce al’ummar Najeriya sun yiwa kalaman sa gurguwar fahimta kan bukatar samun karin jami’an tsaro.

A cewar sa ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara daukan sabbin jami’an tsaro a kasar nan dubu hamsin, ba miliyon hamsin ba kamar yadda wasu ke fada.

Tsohon gwamnan jihar ta Lagos Tinubu ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ya fitar ta hannun mai bashi shawara kan kafafen yada labarai Mr. Tunde Rahman.

A cewar sanarwar Tinubu na nufin gwamnatin ta kara daukan sabbin jami’an tsaro dubu hamsin da suka hadar da jami’an ‘yan sanda da Civil Defence da kuma jami’an Soji, domin inganta sha’anin tsaro a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!