Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Shiru-shiru ba tsoro bane: Martanin sarkin musulmi ga kungiyar CAN  kan nadin sabbin alkalai.

Published

on

Majalisar koli da ke kula da harkokin addinin musulunci ta kasa (NSCIA) ta caccaki kungiyar kiristoci ta kasa (CAN), sakamakon sukar da ta yiwa nadin sabbin alkalai guda ashirin da majalisar kula da harkokin shari’a ta kasa ta yi.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da majalisar ta fitar mai dauke da sa hannun mukaddashin daraktan mulkin majalisar ta NSCIA farfesa Salisu Shehu da kuma sakatare janar na majalisar Arc Haruna Zuberu Usman-Ugwu.

Majalisar ta ce ko da ya ke ba kasafai ta ke son mai da martani ga kungiyar ta CAN kan irin wannan batu ba, amma wannan ya zama wajibi domin fa shiru-shiru ba tsoro bane.

Sanarwar ta ce kwanakin baya majalisar ta bankado yadda aka rika nunawa mabiya addinin musulunci wariya a gidan talabijin na kasa (NTA) wanda tsofaffin hukumomin gudanarwar gidan talabijin din da suka gabata su ka rika yi, bayan da kungiyar ta CAN ta yi wani irin wannan zargin nata na surkulle.

‘‘Wannan rashin kunya ne da cin fuska a rika zargin musulmi da danniya bayan kuma a zahiri al’ummar musulmi sune aka fi dannewa a duk wani lamari na gwamnati a kasar nan, wanda wani tsari ne da tun farko turawan mulkin mallaka suka dora kasar akai’’

 ‘‘Duk wani neman canja lamari yadda ya ke game da nadin alkalan guda ashirin da kungiyar CAN ke yi ba zai samu nasara ba’’

‘‘Sanin kowa ne shugaban kotun daukaka kara mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta yi bayani dalla-dalla kan wannan lamari, da hanyoyin da aka bi wajen zaben alkalan, wanda ta ce, an bi dukkannin ka’idoji da suka kamata ba tare da la’akari da addini ko kabila ko kuma yankin da wani ya fito ba, amma duk da haka, masu neman cin zarafin musulmi da masu fakewa da addini suna biyan bukatun-su sun fake da batun suna cin zarafin mu’’

‘‘Sun ma manta cewa har yanzu al’ummar musulmi duk da cewa su ke da rinjaye a kasar nan amma suke da kaso na marasa rinjaye a kotun daukaka kara’’

‘‘A yanzu haka halin da ake ciki jimillar alkalan da ke kotun daukaka kara guda saba’in ne, arewa da ke da jihohi goma sha tara tana da alkalai 34 yayin da kudanci da ke da jihohi sha bakwai ke da alkalai 36 saboda haka wa aka cuta Kenan?’’ a cewar majalisar koli da ke kula da harkokin addinin musuluncin.

‘‘A bangare guda cikin alkalai guda talatin da shida da ke kudancin kasar nan a kotun daukaka kara guda biyu ne kawai musulmi, wato mai shari’a Habeeb Adewale Abiru daga jihar Lagos da kuma mai shari’a Mistura Bolaji-Yusuf daga jihar Oyo’’

Amma a yankin arewa guda goma sha biyar cikin alkalan guda talatin da hudu duk kiristoci ne, inda yankin arewa maso gabas ke da alkalai musulmi hudu kawai, ya yin da kiristoci ke da guda bakwai, arewa maso tsakiya na da alkalai kiristoci guda bakwai musulmi guda shida, yayin da yankin arewa maso yamma ke da alkalai musulmi guda tara kirista guda daya.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!