Labarai
Yan jarida za su iya taka rawa wajen kawo cigaban al’umma- Halilu ‘Dan Tiye
Kwamishinan yaɗa labarai a jihar Kano Baba Halilu Dantiye, ya ce ‘wajibi ne kafafen yaɗa labarai su mai da hankali wajen fito da abubuwan da za su kawo ci gaba musamman a fannonin Ilimi da lafiya da kuma tsaro.
Baba Halilu Dantiye, ya bayyana hakan ne yayin liyafar cin abinci da ‘Yan uwa da abokan arziki suka shirya masa a daren ranar Asabar da nufin tunasar da shi nauyin da aka ɗora masa.
Baba Halilu Dantiye, ya ce ‘akwai tarin ƙalubalen da ya daibaibaye da harkokin yaɗa labarai da suke bukatar ayi musu duba na tsanaki don magance su.
Ya Kuma tabbatar da cewa ‘zai yi iya bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ya yi aiki bisa gaskiya da rikon amana’.
A nasa jawabin wazirin Dutse Alhaji Bashir Dalhatu, ya bayyana cewa matukar sabon komishinan ya yi aiki kamar yadda aka sanshi a baya zai kawo ci gaban da ake buƙata a jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
Wanda yace duba da irin hazaka da kuma son aiki irin na Baba Halilu Dan Tiye ya ganin za’a iya samun cigaba me dorewa a wannan fannin.
Da yake bayyana maƙasudin shirya liyafar Dan malikin Kano Ambasada Ahmad Umar, ya yi fatan Kwamishinan zai yi amfani da shawarwarin da suka bashi tare da sauƙe nauyin daya rataya a wuyansa.
Taron liyafar dai ya samu halartar manyan yan siyasa da shugabanin kafafen yaɗa labarai sai kuma masu rike da sarautaun gargajiya.
Rahoton: Abba Isa Muhammad
You must be logged in to post a comment Login