Labaran Kano
‘Yan kasuwa su kula da tsaftace wuraren sana’ar ku-Hussam Musa Kyari
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci manya da kananan kasuwanni jihar da su kula da tsafce guraren da suke saa’ar su domin kiyaye yaduwar cututtuka a tsakanin al’umma.
Sakataren ma’aikatar muhalli ta jihar Kano Injiniya Hussam Musa Kari ne ya bayyana hakan a yau, a yayin zagayen fuba tsaftar kasuwanni da ma’aikatu gwamanati da ake gudanarwa a karshen kowanne wata.
A ziyarar ma’aikatar muhalli a kasuwar Yan goro dake mariri da Kuma ma’aikatar tsara butane KNUPDA Injiniya Hussam Musa kyari ya bukace su da rika fitar da shara tare da fitar da duk wani abu da bashi da amfani don hana bawa beraye mafaka.
Shugaban kungiyar kasuwar Yan goro da ke mariri Alhaji Yusuf Adamu Ya’u ya bawa ma’aikatar tabbacin Kara kulawa da tsaftar kasuwa.
Da take karbar bakuncin tawagar ma’aikatar muhalli Hajiya mariya Hussain Zubairu daraktan kula da kasuwanni da tsare tsaren su ta bayyana farin cikin ta tare da alwashin Kara jajircewa.
Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa ma’aikatar muhalli ta jihar Kano na sake Kira ga al’umma wajen kula da tsaftar muhalli Wanda Zia taimaka wajen dikile yaduwar cututtuka.