Kasuwanci
‘Yan kasuwar Filin Idi da gwamnatin jihar Kano ta rushe sun shigar da kara Kotu
‘Yan kasuwar Filin Idi da gwamnatin jihar Kano ta rushe sun garzaya zuwa babbar kotun Tarayya dake Kanon, domin ta dakatar da gwamnatin jihar da kwamishinan ‘Yan sanda da kuma Hukumar Tsara Birane da yin tasarrafi da guraran da aka rushe musu.
A Yau Juma’a ne Babbar Kotun Tarayyar karkashin mai shari’a Simon Amobeda ya bayar da umarnin dakatar da yin duk wani tasarrufi da FIlin Idin da aka rushe har sai anzo gaban kotu.
‘Yan kasuwar su kimanin 56, sunce ‘neman Odar daga kotun ya zama wajibi ne bisa zargin yinkurin baiwa wata cibiya daga Saudi Arebiya yin amafani da filin Idin da aka rushe’.
Jim kadan bayan kotun ta bayar da Umarnin ne, Lauyan ‘Yan kasuwar Barista Nura Ayagi, ya ce sun garzaya kotun ne domin tausayawa masu kananan sana’oi da masu kasuwanci a wajen.
Rahoton: Yusuf Ali Abdallah
You must be logged in to post a comment Login