Labarai
Yan kunar bakin wake 3 sun mutu a harin Muna Garage
Tsohon shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno, SEMA, kuma shugaban kwamitin da ke kula da ayyukan agaji a Jihar ta Borno Engr. Satomi Ahmad ya shaida wa manema labarai cewa hare-haren an kai su ne daban-daban har sau uku.
Ya ce jami’an agaji da na tsaro sun kai dauki ga wadanda suka samu raunuka inda aka garzaya da su asibiti.
Jami’in ya kuma ce abun ya faru ne da kusan karfe 9:30 na dare, ko da yake kafin sannan da wajen misalin karfe 7:00, lokacin sallar Magariba, an rika jin kararraki, wadanda ake gani ko na makaman atilare ne na soji.
Rahotanni sun ce bayan kai harin abubuwa sun lafa, mutane suka ci gaba da gudanar da harkokinsu, kafin zuwa lokacin dokar hana fita ta dare wadda ke aiki daga karfe goma da rabi na dare a birnin, ko da yake yankin da abin ya faru suna da lokacinsu na dokar daban, kasancewar yankin na bayan gari ne.
Wannan dai shi ne karo na kusan 13 da ake kai harin kunar bakin-wake a yankin na Muna Garage, kuma na biyar a cikin wannan shekarar ta 2018.