Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar agaji ta Red Cross ta hada mahaifiya da ‘yarta mai shekaru 7, shekaru 4 bayan rabuwar su sakamakon harin Boko Haram

Published

on

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ICRC, ta ce, ta hada wata mahaifiya mai suna Aishatu Shehu tare da ‘yarta mai shekaru bakwai mai suna Amina, shekaru hudu bayan rabuwar su sakamakon hare haren Boko Haram.

Wata babbar jami’ar kungiyar ta Red Cross a jihar Adamawa Pamela Ongoma ce  ta bayyana haka ga manema labarai.

Ta ce hakan ya faru ne sakamakon amfani da hotunan mutanen biyu da suka yi.

Tace Amina ta rabu da mahaifiyarta ce a shekarar 2014 lokacin ta na ‘yar shekara uku bayan harin da aka kai a Askira Uba da ke jihar Borno.

Pamela Ongoma ta kuma ce Aishatu tana zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Maiha a jihar Adamawa yayin da kuma mahaifiyarta ta ke rayuwa kauyen Dusulu dake karamar hukumar Damboa a garin Borno.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!