Connect with us

Labarai

‘Yan kungiyar  Boko Haram sun kai hari a jihar Adamawa

Published

on

Kungiyar Boko Harama ta kai hari a wani kauye dake karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa.

‘Yan Boko Haram sun dai kai harin da yammacin jiya Litinin yayin da suka yi wa kauyen mai suna Kirchinga tsinki kuma bayan kai harin ne suka cinawa kauyen wuta yak one wasu daga cikin gidajen mazauna yankin.

Wani mazaunin yankin ya shedawa jaridar The Nation cewa ‘yan kungiyar Boko Haram din sun shiga kauyen ne cikin wasu motoci da Babura yayin da suka yi ta harbe-harben iska.

Yayin harbe-harben sun kwashe kayayyakin abinci a cikin shagonan mutane daga bisani kuma suka kone gidaje a gefe guda kuma mutane suka yi ta gudu don tsira da rayukan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!