Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Adam Zango ya nemi sulhu da hukumar tace fina-finai ta Kano

Published

on

Fitaccen jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa Adam A. Zango ya mika wuya tare da neman sulhu da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Jarumin ya wallafa Form din sa na neman iznin hukumar domin cigaba da gudanar da ayyukansa bisa doka da sharudanta a shafinsa na Instagram, inda ya rubuta cewa “an wuce wurin…”.

Izuwa yanzu ‘yan uwa da abokan jarumin na ta bayyana ra’ayoyin su kan batun, ciki kuwa harda fitaccen jarumin nan Ado Gwanja wanda yace da Adam A. Zango “Hakika na fika farin ciki da wannan mataki”.

Wannan mika wuya da Adam A. Zango yayi, za a iya cewa ya kawo karshen dambarwar da aka shafe tsawon lokaci ana tafkawa a baya tsakaninsa da hukumar tace fina-finan ta jihar Kano, wadda har ta kai hukumar taki amincewa ya zo Kano domin kallon shirin Mati a Zazzau.

A wancan lokacin dai Adam Zango ya yanke shawarar kauracewa jihar Kano tare da komawa gudanar da ayyukansa a jihar Legas.
Manazarta kan masana’antar fina-finan Hausa na ganin cewa kawo karshen wannan dambarwa zai iya zamowa silar dinke rikicin dake tsakanin shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Isma’il Na’abba Afakallahu da kuma jaruminnan Haruna Baban Chinedu kasancewar ana ganin rigimar ta yi kamari ne a dalilin hana Adam Zango shigowa Kano.

Koma dai menene yanzu lokaci ne kawai zai iya rarrabewa da baccin makaho.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!