Labarai
‘Yan majalisa a Najeriya na cikin barazanar tsaro – Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba umarnin janye jami’an ‘yan sanda da ke kula da manyan jami’ai wato VIPs.
Akpabio ya bayyana cewa wannan mataki na iya jefa ‘yan majalisa da sauran jami’an gwamnati cikin barazanar tsaro, musamman ganin yadda matsalar rashin tsaro ke ƙaruwa a wasu sassan ƙasar nan.
Sannan ya bukaci shugaban ƙasa da ya yi la’akari da tsaron rayukan ‘yan majalisa da iyalansu, tare da nemo wata hanya da za ta ba su kariya baki ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login