Labarai
‘Yan Majalisar Nijeriya sunki amincewa da siyan jirgin ruwan da Bola Tinubu ya bukata
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis ta yi fatali da bukatar Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ta kashe Naira biliyan 5 daga cikin kwarya-kwaryar kasafin kudin tiriliyan 2.17 wajen sayen jirgin ruwa.
A maimakon haka, majalisar ta bukaci a mayar da kudin wajen kara yawan kuɗin da aka ware domin ba dalibai rance, wanda a baya aka ware wa biliyan 10.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Abubakar Kabir (APC, Kano) ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan da kammala amincewa da kasafin a Abuja
Matakin na ’yan majalisar ba zai rasa nasaba da koke-koken da ’yan Najeriya suka rika yi ba tun bayan bullar labarin, inda suka ce ya zo a daidai lokacin da ’yan kasa ke korafin kuncin rayuwa.
Wanda ya a ce ‘daukar matakin ya zama wajibi la’akari da kudin da aka ware wa daliban a cikin kasafin ya yi kadan’.
Abubakar ya kuma ce kwamitin ya kason da aka ware wa Ma’aikatar Tsaro daga Naira biliyan 476 zuwa 546 sakamakon ƙaruwar kalubalen tsaro.
Shugaban kwamitin ya kuma ce ‘sun duba tare da amincewa da batun kara mafi ƙarancin albashin ma’aikata domin mika shi ga bangaren zartarwa’.
Sai dai ya ce ‘za su tabbatar suna sanya idanu ga bangaren zartarwa domin ganin sun yi abin da ya dace’.
Amma daga bisani Fadar Shugaban Kasa ta ce jirgin ruwa ba na amfanin Tinubu ba ne, na Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ne.
You must be logged in to post a comment Login