Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hadiza Gabon ta maka wani mutum a Kotu bisa zarginsa da cin zarafinta

Published

on

Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu, wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, ta maka wani mutum Bala Musa, ma’aikacin gwamnati, a gaban wata kotun Majistare da ke zamanta a Titin Daura, a jihar Kaduna bisa zargin ɓata mata suna.

Jarumar, ta shigar da ƙarar ta hannun lauyanta, Mubarak Sani, ta na mai da’awarr cewa ta fuskanci munanan kalamai da kuma cin mutunci daga jama’a saboda sharrin da wanda ake kara ya yi mata.

Ta Kuma ce, ‘mutane musamman a shafukan sada zumunta na Intanet sun kira Gabon da macuciyar da ta riƙa cin kuɗaɗen Musa ta kuma ƙi aurar sa’, zargin da aka tabbatar da cewa karya ne.

Wanda ake tuhumar, ta bakin lauyansa, Murtala, ya musanta zargin.

Alkalin kotun, Shamsudeen Sulaiman, ya tambayi lauyan mai karar ko suna da shaidu, inda su ka amsa da cewa suna da su.

A don haka, Alkalin kotun ya bayar da belin wanda ake kara da sharadin ya gabatar da wasu amintattun mutane biyu mazauna jihar Kaduna kuma dole ne su kasance ma’aikatan gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa, Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba domin mai karar ta gabatar da shaidu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!