Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

‘Yan mari 36 sun shaki iskar ‘yanci a Kano

Published

on

A yammacin yau Laraba ne dai wani kwamiti da gwamnatin jihar Kano ta kafa da zai tsaftace makarantun gyaran tarbiyya wato na ‘yan mari ya kai sumame makarantar Daiba dake unguwar Rijiyar Lemo a nan Kano.

Kwamitin wanda ya hadar da jami’ai daban-daban ciki har da dakarun Hisbah sun tarwatsa makarantar tare da kwashe ‘yan marin har ma suke kira ga iyayen yaran da su zo hukumar Hisbah domin karbar ‘ya’yan su, bias zargin ana azabtar da yaran.

Wakilin mu Yusuf Ali Abdallah ya rawaito mana cewa Shugaban kwamitin Mallam Muhammad Tahar Baba Impossible ya bayyanawa Freedom Radio cewa wannan kwamiti na su yana bibiyar wadannan makarantu domin kawo gyara, amma abin mamaki lokacin da yaje kai ziyara wannan makaranta sai ya tarar da lamarin ya ta’azzara, hakan ya tilasta musu kwashe dukkanin ‘yan marin guda 36.

Hotunan wasu daga ‘yan marin da aka tseratar:

Baba Impossible ya bayyana cewa gwamnatin Kano bata son ta kai ga an yiwa makarantun irin yadda aka yiwa sauran jihohi, don haka ne ta kafa wannan kwamiti.

Izuwa yanzu dai kwamitin ya ziyarci makarantun da dama a nan Kano.

Shima a nasa bangaren shugaban makarantar Sheikh Tijjani Sharif Saleh ya bayyana cewa jami’ai sun zo sun duba tsarin yadda suke gudanar da makarantar ne kawai, sannan an nemi su daina amfani da mari, shi ne daga nan aka taho dasu zuwa hukumar Hisbah.

Rubutu Masu Nasaba:

Ko mene ne makomar ‘yan marin da ake sakowa?

‘Yan mari sun shaki iskar ‘yanci a Kano

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!