Labarai
Hisbah ta cafke masu Kanjamau
A shekarun baya ne hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kai samame a Kwanar Gafan dake kasuwar ‘yan Timatiri a nan Kano.
A yayin samamen dai hukumar ta Hisbah ta kama wasu da ake zargin suna zaman dadiro da suka kai sama da tamanin 80 ciki har da Maza da Mata kuma a cikin akwai masu dauke da cuta mai Karya garkuwa jiki ta HIV/AIDs.
Sai ga shi kwatsa ham hukumar ta Hisbah ta sake kai irin wannan samamen kuma ta sami nasarar kamo fiye da mutane casa’in da uku 93, a ‘yan Tuwo-Tuwo dake yankin Badume a yankin karamar hukumar Bichi.
Daga cikin wadanda aka amma akwai Mata Ashirin da uku 23 dake dauke da cutar yayin da kuma Maza hudu 4 suma ke dauke da cutar.
Akasarin matan da mazan kan yi aure ba tare sun san cewar suna dauke da wannan cutar ba mai karya garkuwar jiki.
Batutuwa masu nasaba
Yadda hukumar Hisbah ta sauke ‘yan kwamitin gudanarwarta
Hukumar Hisbah ta kama mabarata anan Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben barasa 196,400
Sai dai bayan da hukumar ta Hisbah ta sanya likitoci suka yi wa matan gwaji, sun tabbatar da cewar Mata Ashirin da Uku na dauke da cutar mai karya garkuwar jiki.
Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheik Muhammad Harun Ibini Sina yace bayan da likitocin suka gudanar da tantancewar ne, sai suka tabbatar wa hukumar cewa suna dauke da cutar mai karya garkuwar jikin.
Guda daga cikin Matan wadannan aka kama tace suna gudanar da sana’ar su ne na saida Tuwo a Badumen lokacin da dakarun Hisban suka kai samame .
Amma dai wani abun mamaki shi ne, Mazan da aka kama su biyar sun san cewar suna dauke da cutar, kuma suka cigaba da gudanar da sana’ar su ba tare da jin tsoron yada cutar ba.