Connect with us

Labarai

Yan Najeriya 570 aka kashe daga Janairu zuwa Afrilu- NHRC

Published

on

Hukumar kare haƙƙin Dan-adam ta Najeriya ta ce adadin mutum ɗari biyar da saba’in (570) aka kashe a watan Afrilun bana.

 

Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wani sabon rahoto da ta fitar.

 

Haka kuma, ta ce, mutane ɗari biyu da saba’in da takwas (278) aka yi garkuwa da su daga alƙaluman da ta tattara, a baya baya nan.

Ta cikin jawabin da ta wallafa a  shafinta na intanet, hukumar ta ce, ta tattara alƙaluman ne daga koken da ta samu na keta haƙƙin ɗan adam daga ofisoshinta da ke sassan Najeriya.

 

Rahoton dai ya yi nazari ne tun daga watan Janairun bana har zuwa watan Afrilu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!