Labarai
‘Yan Najeriya na fuskantar karancin abinci – kungiyar FAO
A baya bayan nan ne wata kungiyar majalissar dinkin duniya dake lura da abinci da hakar noma da ake kira da “The food and agriculture organization” ta gudanar da bincike dake bayyana cewa sama da ‘yan Najeriya miliyan hudu da dubu dari biyu ne ke fuskantar matsanancin karancin abinci dake gina jiki a kasar nan.
Binciken wanda aka yi a jihohi goma sha bakwai dake Arewacin kasar nan, ya nuna cewar, za’a fuskanci matsanancin karancin abincin dake gina jiki daga watan Yuni zuwa watan Disambar shekara ta 2020 matukar ba a dauki matakin kare afkuwar hakan ba.
Wakilin mu Aminu Abdullahi Ibrahim daya bibiyi binciken rahoton ya rawaito mana cewar,an dai fara gudanar da binciken ne a shekara ta dubu biyu da 2016 da jihohi takwas a Arewacin kasar nan inda daga bisani aka karasu zuwa goma sha shida da nufin gano jihohin da suke fuskantar matsalar ta karancin abincin dake gina jiki don janyo hankalin masu ruwa da tsaki domin magance matsalar.
Ministan kwadago ya sha alwashin fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi
Ranar Abinci ta duniya: Mai masana suka ce kan wannan?
Abincin Naira 30 ya jawo cecekuce.
Rahotan ya kara cewa jihar Yobe ita ce akan gaba yayin da Borno ta kasance ta biyu sai Adamawa wacce ita ce jiha ta uku da suka fi fama da matsalar ta karancin abincin.
Sai dai rahoton ya alakanta samun rikicin kabilanci da matsalar tsaro da Ambaliyar ruwa da kuma barkewar cututtuka amatsayin ababen dake haddasa matsalar ta karancin abinci a Najeriya.
A nata bangaren gwamnatin tarayya ta bakin minista noma da raya karkara tayi godiya da sakamakon binciken, inda tace zai taimakawa gwamnati wajen ganin ta yi amfani da hanyoyin da suka dace don yaki da yunwa da kuma karancin abinci a kasar nan.
Kan wannan batu ne freedom radio ta jiyo mabanbanta ra’ayoyin wasu mutane a nan Kano.
Wani tsohon soja a nan Kano warrant officer II, Nasiru Muhammad, ya bayyana cewa rashin tsaro da aka alakan tashi da matsalar karancin abinci da ake fama dashi a kasar nan, ya samo asali ne tun a baya, inda yace gwamnati tayi sakaci wajen barin matasa babu aikinyi da rashin kyautatawa ma’aikata wanda hakan ke kara ta azzara matsalar tsaro.
A nasa bangaren wani masani a fanin aikin gona farfesa Musa Tukur Yakasai, yayi tsokaci a kan lamarin inda yace talauci na takarawar gani wajen ta’azara matsalar karancin abincin dake gina jiki.
Malamin ya kara da cewa kamata yayi gwamanati ta bunkasa hanyoyi daban-daban da zasu samar da abincin dake gina jiki bawai maida hankali kan noman shinkafa da sauran kayayyakin hatsi ba.
AMasana da dama a bangaren ayyukan noma da masu ruwa da tsaki na fatan sakamakon wannan bincike zai taimaka don magance matsalar karancin abinci da wasu daga cikin al’ummar kasar ke fuskanta.