Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Akwai yiwuwar samun karancin abinci a jihohi 16 na Arewacin Najeriya-FAO

Published

on

Hukumar kula da Samar da abinci dan inganta ayyukan gona ta duniya FAO ta yi gargadin cewar akwai yiwuwar samun matsananciyar matsalar karancin abinci da za ta shafi kusan mutane miliya 4 a jihohi 16 da ke Arewacin Najeriya

A cewar hukumar ta FAO, da kuma hukumar bayar da agajin abinci ta Majalisar dinkin duniya WFP, matsalar za ta shafi hatta birnin Tarayyar  Abuja, muddin aka gaza daukar matakan gaggawa.

FAO da kuma WFP sun ce jihohin da matsalar za ta shafa sun hada da  Bauchi, Benue, Gombe, Jigawa, Plateau, Niger, Kebbi, Katsina, Kaduna, Taraba, Zamfara, Sokoto, Kano, Yobe, Borno da kuma Adamawa.

A don haka ne hukumomin biyu suka shawartar hukumomin a kasar nan da kuma jihohin da al’amarin zai sahafa da su dauki matakin gaggawa domin kaucewa fadawa cikin matsalar ta yunwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!