Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar GREKIN ta nemi gwamnatoci da su inganta tituna

Published

on

Shugaban kungiyar Greater Kano Initiative GREKIN Kwamared Kabiru Marmara yayi kira ga gwamnatin tarayya da sauran Gwamnatocin jihohin kasar nan dasu kawo karshen lalacewar manyan titunan kasar nan sakamakon munanan hadduran da titunan ke haifarwa a Najeria.

Kabiru Marmara ya ya bayyana hakan ne lokacin gudanar da tattakin da kungiyar ta gudanar domin tunawa da ranar wadanda suka gamu da matsalar hadari a duniya da majalisar dinkin duniya ta ware kowacce ranar  sha bakwai ga watan Nuwaban kowacce shekara domin tunawa dasu.

Kwamared Kabiru Marmara ya kara da cewa kawo karshen lalacewar manyan titunan kasar nan ne kadai zai rage yawan mace – macen dubban mutane da Najeria ke fama dashi , a don haka ne yace yana kira ga gwamnatoci suyi gaggawar kawo karshen wannan gagarumar matsala domin rage yawan mutuwar mutane.

‘Yan Najeriya na fuskantar karancin abinci – kungiyar FAO

Rundunar sojan sama ta lalata maboyar kungiyar ISWAP

Kungiyar kishin al’ummar Kano za ta gina cibiyar fasaha

Shugaban Kungiyar ya nanata cewa sakamakon binciken da suka gudanar a Hukumar kashe gobara ta Kano da kuma sauran Chaji offisoshin ‘yan sanda na Kano sun gano suna fuskantar matsalar karancin jini wanda hakan yasa kungiyar zata fara ba yarda jini kyauta ga wadannan hukumomi domin tallafawa rayuwar su.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa kungiyoyi masu zaman kansu da sauran jami’an tsaro da dama ne suka halarci tattakin domin wayarwa da mutane kai don tallafawa wadanda suka gamu da  matsalar Haddura iri daban – daban a fadin kasar nan.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!