Labarai
Rundunar Yan sandan Gombe ta musanta samun yan bindiga a Jihar
Rundunar ‘yan sanda a jihar Gombe ta yi watsi da ikirarin cewa akwai yan bindiga a wasu sassan jihar.Tun a ranar Talatar data gabata ne dai kwamandan rundunar tsaron farin kaya ta Civil Defence a jihar Gwambe Muhammad Mua’azu, ta cikin wani faifan bidiyo daya karade kafafen sada zumunta, aka jiyo shi yana cewa sun samu rahotanni na sirri dake nuni da yadda yan bindigar suka bulla, tare da fara neman wadanda zasu hada kai da su a matsayin yan leken asiri da aka fi sani da imfoma.
To saidai ta cikin wata takarda da rundunar yansandan ta fitar jiya Juma’ah mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’ah na rundunar Mahid Abubakar, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Gombe Hayatu Usman, ya ce ikirarin bashi da tushe bare makama.
Haka kuma rundunar ta bukaci al’ummar jihar dasu kwantar da hankulansu, tare da bada rahoton bullar duk wata bakuwar fuska da basu gamsu da ita ba domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin su.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu
You must be logged in to post a comment Login