Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An maida yaran da aka sace daga jihar Gombe zuwa Anambra – ‘Yan sanda

Published

on

Yara 11 da aka sace su ‘yan asalin jihar Gombe kuma aka yi safarar su zuwa jihar Anambra an maida su hannun rundunar ‘yan sandan jihar ya yin da aka kasa gano yan uwa da dangin su.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Anambra ta bayyana cewar, kawo yanzu yara 18 ne aka kasa gano dangin su da ‘yan uwan su ‘yan asalin jihar ta Gombe.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ana zargin wata mace mai sauna Hauwa Usman da sace yaran a ranar 20 ga watan Okotoban bara a jihar Gombe kana kuma ta yi safarar su zuwa jihar Anambra.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Gombe DSP Mohammed Haruna  ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ne ya nuna cewa ana zargin Hauwa Usman da sace yaran.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!