Connect with us

Labarai

‘Yan sanda a Kano sun fara bincike kan kone wani magidanci da iyalansa

Published

on

‘Yan sanda a Kano sun fara bincike kan kone wani magidanci da iyalansa

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP. Ahmed iliyasu ya bada umarnin fara bincike domin gano wasu da ba’a san ko su wanene ba, da ake zargin sun kulle kofar wani gida ta baya, sannan suka cinnawa gidan wuta a unguwar Gayawa dake yankin karamar hukumar Ungogo.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida mana cewa al’amarin ya faru ne da misalin karfe biyu na daren jiya Talata, kuma tuni suka fara binciken al’amarin, kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda ya bada umarni, shaidun gani da ido sun shaidawa Freedom Radio cewa sunyi iya kokarinsu wajen ganin an balle kofar amman abin yaci tura.

Tuni dai jami’an hukumar kashe gobara suka dauki gawargawarkin magidancin da matarsa da kuma ‘yar sa wanda tuni sun rigamu gidan gaskiya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!