Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Sanda a Kano sun kama wasu mutane 29 da take zargin ‘yan daba ne

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wasu batagari da take zargin ‘Yan Daba ne wanda yawansu ya kai 29 a dai-dai lokacin da ake gudanar da taron Takutaha dauke da muggan makamai a nan Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai da yammacin jiya Juma’a.

SP Haruna Kiyawa ya kara da cewa ‘babban Sifeton rundunar ‘yan sandan kasar nan Kayode Emetekon ne ya bada umarnin kara tsaurara matakan tsaro a fadin kasar nan a lokacin gudanarda tarukan Maulidi domin ganin anyi taron cikin koshin lafiya’.

Freedom Radio ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ‘da zarar rundunar ta kammala gudanarda bincike akan matasan da ake zargi zasu gurfanar dasu a gaban Kotu’.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!