Labarai
‘Yan sanda a Najeriya sun tsare Alwan Hassan bisa zargin Barau Maliya da hana tabbatar da nadin Ramat a NERC

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ’yan sandan Najeriya ta tsare Alwan Hassan kwanaki kaɗan bayan da ya zargi mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da yin katsalandan wajen hana tantancewa da tabbatar da nadin Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban Hukumar Kula da Lantarki ta Kasa (NERC).
Wani rahoto daga DAILY NIGERIAN ya bayyana cewa an tsare Alwan Hassan ne a ranar Juma’a bayan ya amsa gayyatar da Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar (FCIID) da ke Abuja ya aike masa.
A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike kan zargin da Alwan ya yi, tare da tantance tasirin da maganganunsa suka haifar a siyasar jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login