Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Sanda a Zamfara sun ceto mutane 9 daga hannu masu garkuwa da mutane

Published

on

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta samu nasarar ceto mutane tara da masu garkuwa da mutane suka sace, tun a ranar 11 ga watan Afrilun da muke ciki a karamar hukumar Tsafe.

Mai magana da yawun rundunar CSP Muhammad Shehu ne ya tabbatar da hakan a Gusau babban birnin jihar, inda ya ce, an ceto mata bakwai da maza biyu daga hannun yan bindigar a jiya.

A cewarsa, ‘an samu nasarar ceto su ne, biyo bayan samun bayanan sirri da aka yin a wurin da yan bindigar suka boye su, kuma aka bi hanyoyin ceto su cikin nasara’.

CSP Muhammad Shehu ya kuma ce, ‘tuni aka aike da wadanda aka ceto din zuwa asibiti domin duba lafiyarsu, daga bisani kuma aka damka su a hannun iyalansu’.

 

Rahoton: Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!