Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NDLEA ta gano wasu gonakin Wiwi a Katsina

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta gano gonaki uku da ake shuka ganyen wiwi a jihar Katsina.

Mataimakin shugaban hukumar mai kula da harkokin gudanarwa na jihar, Halilu Hamidu ne ya bayyana hakan.y

Yana mai cewa, ‘sun samu nasarar gano gonakin ne bayan samun bayanai daga wasu mutane’.

Hamidu ya kuma ce ‘wannan shi ne karon farko da hukumar ta gano irin wannan gonar a kauyen Sobashi na karamar hukumar Dutsi’.

Ya kuma ce, ‘masu gonar suna amfani da ita wajen shuka tabar ta wiwi amma suna fakewa da noman kayan lambu irinsu tattasai da tumatur, sai dai tuni aka kama mutum daya daga ciki, sannan ana ci gaba da bibiyar sawun sauran abokan huldarsa.

 

Rahoton: Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!