Connect with us

Labarai

Rundunar sojin Najeriya ta yi holin mutane 13 da ake zargin su da hannu wajen bacewar Janar Idris Alkali

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta yi holin wasu mutane 13 da ta ke zargin suna da hannu wajen bacewar Janar Idris Alkali, wanda ya bata a watan Satumbar da ya gabata.

Kwamandan runduna ta 3 da ta gudanar da binciken Umara Muhammed ya ce za su mikawa rundunar Yan Sanda mutanen da ake zargin domin gudanar da nasu bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamandan ya ce wadanda za’a mikawa Yan Sandan sun hada da wadanda aka samu da makamai da wadanda suka tare motar Janar Alkali da kuma wadanda suka tura ta cikin tafki.

Jami’in ya ce suna da bayanai kan wasu da ake zargin suna da hannu cikin lamarin amma kuma suka gudu inda ya ce da zarar bincike ya tabbatar da zargin da ake musu to za su girbi abin da suka shuka.

Tun a watan oktobar da ya gabata ne dai iyalan Marigayi janar Alkali suka sanar da bacewar sa, daga baya kuma rundunar sojin kasar nan ta ce ta gano motar sa a cikin wani tafki da ke yankin Duradi a jihar Filato.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,889 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!