Labarai
‘Yan sanda sun cafke mutane 32 da ake zargi da ta’addanci a jihar Kwara

’Yan sanda sun cafke mutane 32 da ake zargi da aikata ta’addanci a wasu yankunan Jihar Kwara sakamakon wani samame da suka kai a maboyar masu laifi da ke cikin dazuka.
wannan na cikin sanarwar da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara SP Adetoun Ejire Adeyemi ta fitar a ranar Talata 10 ga Maris 2026.
Sanarwar ta ce an kama mutanen ne bayan wani aiki na tattara bayanan sirri da rundunar ’yan sanda ta gudanar tare da hadin gwiwar tawagar sashen leƙen asirin rundunar a yankunan Kaiama, Patigi, Gbugbu, Tsaraji, Babanla da Awi.
Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin na cikin kungiyoyi daban-daban da ke da hannu a garkuwa da mutane, satar shanu da sauran manyan laifuka, inda suke amfani da dazuka a matsayin maboya.
Sanarwar ta kara da cewa cikin wadanda aka kama akwai wasu ’yan kasashen waje guda biyu daga Jamhuriyyar Nijar da ake zargin suna hada kai da kungiyoyin masu laifi wajen aikata laifuka a yankin.
Haka kuma rundunar ta kama wani mutum mai suna Umar Mohammed daga Jihar Filato da ake zargi da samar da na’urorin sadarwa ga masu laifin.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin yayin da ake kokarin kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci a yankin.
You must be logged in to post a comment Login