Connect with us

Labarai

‘Yan sanda sun yi holen wadanda ake zargi da aikata laifuka a Kano

Published

on

Rundunar ‘yansandan jihar Kano tayi holin wadanda take zargi da aikata laifuka daban-daban daga ranar tara ga watan tara na shekarar 2020 zuwa Sha shida ga watan nan da muke ciki a yau juma’a.

A cewar rundunar ‘yan sandan ta Kano ta bakin mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wani taron manema labarai da rundunar ta gudanar da yammacin yau juma’a.

DSP Abdullahi Haruna ya kara da cewa cikin wadanda suka kama da aikata laifukan akwai masu garkuwa da mutane, fashi da makami, da dilolin kwayoyi  tabar wiwi buhu-buhu da ‘yan yahu-yahu, ‘yan damfara da kuma masu bokanci na karya.

‘Yan sanda a Bauchi sun yi holen wasu mutane da ake zargin su da cin zarafin mata

Buhari ya sanya hannu kan dokar ‘yan sanda

Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma kara da cewa yanzu haka rundunar ta damu nasarar cafke masu satar wayoyin jama’a sama da mutane sittin da daya sakamakon cigaba da yawaitar samun satar wayoyi a fadin jihar Kano.

Wakilin mu na Kotu da ‘yan sanda Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa rundunar tayi nasarar cafke wani matashi daya kware wajen satar baburan mutane wanda izuwa yanzu ya saci babura mai kafa biyu sama da guda dari biyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!