Labarai
’Yan Sanda Sun Dakile Harin ’Yan Bindiga a Zamfara

Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da dakile wani yunkurin ’yan bindiga da suka yi na tare babbar hanya a jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Disamba, 2025.
Sanarwar ta ce jami’an sashen hana garkuwa da mutane na rundunar, ƙarƙashin jagorancin ASP Aliyu Bilyaminu Koko, sun samu sahihan bayanan sirri cewa wasu ’yan bindiga sun tare hanyar Tsafe zuwa Yanwarin Daji.
Bayan samun bayanan, jami’an suka gaggauta kai ɗauki zuwa wajen, inda suka yi artabu da ’yan ta’addan. Artabun ya yi sanadiyyar jikkatar wasu daga cikin ’yan bindigar da suka tsere zuwa cikin daji.
Rundunar ta ce an kama mutum guda mai suna Umar Alhaji Bukar, wanda aka fi sani da Bingil, bayan da ya miƙa wuya ga jami’an tsaro.
Rundunar ’yan sandan ta jinjinawa jami’anta bisa jajircewa da kuma al’ummar da suka bayar da gudummawa ta hanyar kai rahoton bayanan sirri, tare da ƙara jaddada buƙatar ci gaba da haɗin kai domin tabbatar da tsaro a jihar.
You must be logged in to post a comment Login