Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun kama masu bayar da bayanan sirri ga ‘yan ta’adda – SOJOJI

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta Operation Sahel Sanity sun yi nasarar cafke wadanda ake zargin suna kaiwa yan bindiga bayanan sirri tare da taimaka musu wajen siyo abinci su 22 a jihohin Katsina da Zamfara.

Daraktan yada labarai na rundunar sojin Benard Onyeuko ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Onyeuko ya ce, a yayin sumamen da rundunar ta kai maboyar ‘yan tada kayar bayan, tayi nasarar ceto makiyaya 40 da ‘yan tada kayar baya suka yi garkuwa da su tare da lalata maboyar ta su.

Sanarwar ta kara da cewa an yi nasarar kama mutanen ne a jihohi biyu na kasar nan, tun daga ranar biyar ga watan Agusta zuwa sha daya ga watan.

Kazalika rundunar ta ceto wata mata da ake kyautata zaton tana da aure wadda kuma take kai bayanan sirri ga yan tada kayar baya a jihar Katsina tare da siyar musu da dabbobin da suka sace a kasuwa don siyo musu kayan bukata.

Ta cikin sanarwar dai, Onyeuko ya kara da cewa, rundunar ta samu nasarar kashe daya daga cikin yan ta’addar, yayin da wasu da dama suka tsere wanda hakan ya bada nasarar kwashe makaman da suke amfani da su, da suka hadar da bindigogi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!