Labarai
Yan sanda sun kama wanda ake zargi da kai wa yan bindiga alburusai a Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta kama wani mutum da ta ke zargi da safarar alburusai ga yan bindiga tare da samunsa da harsasai masu rai guda 800 da aka boye su a cikin tankin mai na babur.
Rundunar ta bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa, jami’inta na hulda da jama’a DSP Yazid Abubakar, ya fitar.
Sanarwar ta ce, an kama wanda ake zargin mai suna Mannir Adam, mai shekaru 25, mazaunin kauyen Yan-kuzo da ke karamar hukumar Tsafe, a ranar 10 ga watan nan da muke ciki na Maris da misalin karfe 7:50 na dare a kan babban titin Gusau zuwa Funtua a wani shingen binciken ababen hawa.
Haka kuma, sanarwar, ta ruwaito cewa, jami’an ‘yan sanda da ke aikin sintiri sun tare wanda ake zargin ne yayin da ya ke tuka babur kirar Boxer mai launin ja, inda bayan bincike suka gano alburusan da aka boye a tankin man babur din.
Rundunar ta kuma bayyana cewa, Binciken farko ya nuna wanda ake zargin na kan hanyarsa ne daga Unguwar Bawa a karamar hukumar Saminaka ta Jihar Kaduna, zuwa kauyen Kucheri da ke karamar hukumar Tsafe a Zamfara.
You must be logged in to post a comment Login