Labarai
Yan-sanda sun kama mutumin da ke safarar babura ga ‘yan bindiga a dazukan jihar Zamfara.
Rundunar ‘yan-sandan jihar Kano ta ce ta kama wani magidanci da ya ke wa ‘yan ta’addan da ke ta’asa a dazukan jihar Zamfara safarar babura kirar Boxer da aka haramta amfani dasu a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ta cikin shirin ‘Dan-sanda abokin kowa na tashar freedom radio da ya gudana da safiyar Lahadi 21/03/2021.
Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce da fari magidancin ya sayi babura guda biyu kirar boxer da aka hana amfani da su a jihar ta Zamfara, wanda a binciken da su ka yi, sun gano mutumin ya sa yi babura guda sittin irin su da yake sauya musu kama sannan a sasu a cikin kwali ana fita da su zuwa jihar ta Zamfara.
Ya kuma ce mutumin yana shigar da baburan zuwa dazukan dake yankin jihar ta Zamfara domin kai wa ‘yan bindigar.
Abdullahi Kiyawa ya ce a binciken da suka fara ya tabbatar musu da cewa akwai mutumin da yake hadawa ‘yan ta’addan baburan a cikin dazukan.
You must be logged in to post a comment Login