Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan Sanda sun kama Wani mutum da sassan jiki a gidansa

Published

on

Rundunar ƴan sanda reshen Jihar Oyo ta kama wani Malami mai shekaru 45 bisa zargin mallakar sassan jikin mutum ɗanye cikin makon nan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sufurtanda Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan a Shalkwatar rundunar da ke Ibadan, yayin da gabatar da wanda ake zargi.

Ya ƙara da cewa ƴan sanda sun kama mai laifin ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2023 da misalin karfe 10:00 na safe a unguwar Ogbere-tioya, Ibadan

Rundunar ƴan sandan ta ci karo da malamin ne bayan gudanar da bincike a tsanake tare da bin diddigi a kusa da yankin Ogbere-tioya, Ibadan, dake ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Ona-ara.

Osifeso ya yi zargin cewa an samu nasarar cafke shi ne biyo bayan rahotannin sirri da aka samu daga jamaa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!