Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sandan Kano ta ja kunnen masu shirin Zanga-zanga

Published

on

Rundinar ‘yan sandan jihar Kano ta sha alwashin cafkewa tare da gurfanar da dukkan mutanen da suka fito domin gudanar da duk wani gangami da sunan gudanar da Zanga-Zanga a fadin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundinar SP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan, yayin da yake zantawa da freedom Radio a daren Lahadin nan.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kuma bai wa al’umma tabbacin cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta dauki matakan da suka dace, tare da baza jami’ansu lungu da sako domin tabbatar da tsaro a fadin jihar.

Haka kuma, ya ja hankalin ‘yan siyasa da magoya bayansu da su bayar da dukkan gudunmawar da ta dace wajen tabbatar da zaman lafiya.

AKI

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!