Kiwon Lafiya
Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 2 a fadowar ginin Anambra
Rundunar yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon fadowar wani gini a yammacin jiya laraba a garin Onitsha.
Mai magana da yawun rundunar, Haruna Muhammad ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a AwKa babban birnin jihar.
A cewar sanarwa, ginin da ke lamba 9 a kan titin Ezenwa a garin na Onitsha ya fado ne da misalin karfe 3:00 na yammacin jiya Laraba, kuma mallakin wani mutum ne mai suna Barista Ikebu.
Sanarwar ta kuma ce, tuni ‘yan sanda da masu bada agajin gaggawa suka kai dauki ga wadanda abin ya shafa, kuma an garzaya da su zuwa babban asibitin jihar da ke garin na Onitsha.