Connect with us

Kiwon Lafiya

Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 2 a fadowar ginin Anambra

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon fadowar wani gini a yammacin jiya laraba a garin Onitsha.

Mai magana da yawun rundunar, Haruna Muhammad ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a AwKa babban birnin jihar.

A cewar sanarwa, ginin da ke lamba 9 a kan titin Ezenwa a garin na Onitsha  ya fado ne da misalin karfe 3:00 na yammacin jiya Laraba, kuma mallakin wani mutum ne mai suna Barista Ikebu.

Sanarwar ta kuma ce, tuni ‘yan sanda da masu bada agajin gaggawa suka kai dauki ga wadanda abin ya shafa, kuma an garzaya da su zuwa babban asibitin jihar da ke garin na Onitsha.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,008 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!