Labarai
Yan sandan Hong Kong sun cafke wani fasinja bisa yunkurin bude kofar jirgin sama

‘Yan sandan Hong Kong sun cafke wani fasinja bisa laifin yunkurin bude kofar jirgin sama, lokacin da yake tsaka da tafiya a sararin samaniya, bayan taso wa daga birnin Boston na kasar Amurka, a kan hanyar zuwa Hong Kong.
Kamfanin jirgin mai suna Cathay Pacific, ya ce a yayin faruwar balahirar, babu wani fasinja ko ma’aikacinsa da ya samu rauni, kuma jirgin ya sauka lafiya.
Tuni ‘yan sandan suka kaddamar da bincike bayan kama matashin da ake zargi da wannan katobara, mai shekaru 20 ‘dan asalin kasar China.
You must be logged in to post a comment Login