Labarai
‘Yan-sanda sun kama mutane 20 da zargin sata da safarar miyagun kwayoyi

Rundunar yansandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane kusan 20 bisa zarginsu da aikata laifukan sata da kuma safarar miyagun kwayoyi.
Bayanin hakan na kunshi ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar SP Lawan Shisu Adam ya fitar harma ya yiwa Freedom Radio karin haske.
SP Shisu ya kara da cewa Rundunar ta sake samun nasarar kama wasu matasa da ake zargi da satar Shanu da Babura da kuma mota a kananan hukumomin Hadeja, Guri da kuma Kiyawa da sauran sassan jihar
Kazalika ya bukaci hadin kan al’umma dasu ci gaba da baiwa jami’an tsaro ingantattun bayanan duk wani motsi da basu gamsu da shi ba.
You must be logged in to post a comment Login