Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Shi’a sun yi bikin Easter da kiristoci a cocin katolika

Published

on

Kungiyar mabiya shi’a bangaren Zakzaky sun gudanar da bikin Easter da mabiya addinin kirista a wani coci da ke birnin Yamai a jamhuriyar Nijar.

Rahotanni sun ce ‘yan shi’ar wadanda suka je cocin na katolika su hamsin sun taya mabiya addinin kirista murnar bikin na Easter.

Kaso casa’in da tara na al’ummar kasar Jamhuriyar Nijar mai dauke da mutane miliyan ashirin da uku da dubu ashirin da uku musulmi ne yayin da kiristoci ke da kaso daya.

Bayanai sun tabbatar da cewa kusan kashi goma cikin dari na al’ummar musulmin kasar ta Jamhuriyar Nijar mabiya shi’a ne.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!