Labaran Kano
Yan siyasa na amfani da inconclusive ne domin cimma wata bukata ta su – Farfesa Fagge
Masanin kimiyyar siyasar nan na jami’ar Bayero dake nan kano farfesa kamilu sani Fagge Yace yan siyasa na amfani da inconclusive ne domin cimma wata bukata tasu ta kashin kai.
Farfesa Fagge ya kuma ce inconclusive ba sabon abu bane a siyasar kasarnan,sai dai a lokutan baya ana amfani da ita ne ta hanyoyin da suka da ce.
Farfesan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala shirin Barka da hantsi na freedom Radio.
“An kafa dokar inconclusive da kyakkyawar manufa domin tantance hakikanin wanda yayi nasara a zabe,sai dai a yanzu ana amfani da ita domin biyan bukatar kai wanda hakan ke barazana wajen haddasa tashe tashen hankali a tsakanin al’umma”.
Farfesa Fagge ya kuma ce mutane su guji kada kuri’a ga duk wanda ya basu kudi ko wanda ke bangar siyasa.
You must be logged in to post a comment Login