Labarai
‘Yan ta’adda sun kai mummunan hari a sansanin jami’an Civil Defence

Wasu yan ta’adda sun kai hari wani sansanin jami’an tsaro na Civil Defence da ke kauyen Ibrahim Leteh da ke kan hanyar Wawa Lumma a karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja
Rahotanni sun bayyana cewa Maharan sun zo su da yawa Inda suka bude wuta kan jami’an tsaron da misalin karfe 4 na safiyar Talata lamarin daya tilastawa wasu daga cikin jami’an tserewa domin tsira da rayuwar su
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa yan ta’addan sun tafi da wasu daga cikin bindugu na jami’an Civil Defence din
Sai dai mai magana da yawun rundunar tsaron ta Civil Defence a jihar ta Neja Abubakar Rabi’u, ya ce, su na ci gaba da buncike domin har yanzu ba su tantance gaskiyar abinda ya faru ba.
You must be logged in to post a comment Login