Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan kungiyar vigilante 20 a jihar Niger

Published

on

Wasu yan bindiga sun yiwa jami’an vijilante kwanton bauna a kauyen Kotonkoro da ke karamar hukumar Mariga, ta jihar Neja tare da kashe mutum 20.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun kai harin ne a daren larabar da ta gabata a sansanin sojoji, inda kuma suka kashe soja daya tare da jikkata wasu da dama.

Kwamandan ‘yan vigilante a karamar hukumar ta Mariga, Abu Hashimu, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa 16 daga ciki an kashe sune nan take ya yin da wasu guda hudu aka harbe su lokacin da suke kokarin tserewa.

Wannan hari dai na zuwa ne sati uku bayan da gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya kai wa ‘yan kungiyar ta vigilante ziyarar karfafa gwiwa tare da tabbatar musu cewa zai samar musu da manyan makaman da za su rika amfani dasu yayin tunkarar ‘yan ta’adda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!