Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

‘yan wasan jihar Kano sun samu nasara a Ramat cup

Published

on

An kammala gasar kofin matasa na kasa ‘yan kasa da shekaru 16, na Ramat cup Wanda aka fi sa ni da (YSFON) Karo na 36, a yammacin jiya, a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata dake nan Kano.

Gasar wadda aka shafe kwanaki 6 ana fafatawa, jihar Kano ce ta samu nasara akan takwarar ta jihar Lagos da ci 2-1, a wasan karshe Wanda hakan ya bata damar kare kambunta. 

Tunda fari dai jihar Kano ta samu damar zura kwallayenta guda 2 ta hannun ‘yan wasa Hamza Rabiu da kuma Usman Auwal, ya yin da Dan wasa Kumasi Moses, ya ramawa jihar Lagos kwallo daya tilo. Hakan ya baiwa yan wasan jihar nan damar lashe gasar, inda Lagos ta zo na biyu sai kuma jihar Kwara sa ta kare a matsayi na uku, a gasar da jihohi 23 suka fafata.

Da yake jawabi a yayin rufe gasar Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa ‘yan wasan jihar Tare da yin alkawarin ci gaba da daukar nauyin gasar, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Shima a nasa bangaren mai horar da ‘yan wasan kungiyar Moses Obioma (Zico) ya bayyana jin dadin sa da nasarar da ya jagoranci kungiyar.

A yayin gasar dan wasa Yusuf Pantami, daga jihar Barno shi ne yafi  zura kwallo da kwallaye 6, ya yin da aka zabi Mubarak Gatta, daga jihar Lagos a matsayin Dan wasa mafi hazaka a gasar, sai mai tsaron raga mafi karsashi a gasar daga jihar Lagos wato Oyenuga Faruq.

Kungiyar yan wasan ta jihar Kano ta samu kyautar zunzurutun kudi naira dubu dari da hamsin, sai jihar Lagos da naira dubu dari, jihar Kwara ta tashi da naira dubu 50, a yayin rufe gasar dai a yammacin jiya, an yi gudun yada kanin wani (Famfalaki) na tseren mita 100, inda jihar Kaduna tayi na daya, sai jihar Rivers a matsayi na biyu inda Jihar Nasarawa ta kare a matsayi na uku da lambar tagulla.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!