Connect with us

Labaran Wasanni

Najeriya zata doke kasar Argentina a gasar cin kofin duniya-Alex Iwobi

Published

on

Dan wasan Najeriya mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Alex Iwobi ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Najeriya zata doke takwararta ta Argentina a gasar cin kofin duniya wanda za’a yi a kasar Rasha tsakanin watan Yunin da Yulin shekar da muke ciki.

Najeriya da Argentina na rukunin daya ne a gasar, kuma za su buga wasan su ne a ranar 26 ga wata Yunin shekarar nan da muke ciki.

Masana harkokin wasanni na ganin cewa Kasar argentina zata nemi daukar fansa kan nasarar da Najeriya ta samu a kanta da ci 4-2 a wasan sada zumunci da suka yi a watan Nowambar shekarar da tagabata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!