Labarai
Yan sandan Jigawa sun kama wadanda ake zargi da fashi

Rundunar yan-sandan jihar Jigawa ta kama mutane 9 bisa zargin aikata laifukan satar Shanu da kayan wutar lantarki da fashi da makami a kananan hukumomi biyar dake jihar.
Da yake yiwa Freedom Radio karin haske kan kamen mai magana da yawun Rundunar SP Lawan Shisu Adam ya ce sun kama mutanen ne ya yin gudanar da jerin wani sumame, bayan karbar korafi kan laifukan da ake zargin wadan da aka kama da aikatawa a kananan hukumomin Malamadori da Ringim da Kazaure sai Jahun da kuma Gwaram.
Kazalika Lawan Shisu ya kara da cewa Rundunar yansandan bisa jagoranci CP Dahiru Muhd na yiwa al’umma godiya kan hadin kan da suke basu wajen gudanar da aikin su wadda ya yi fatan su ci gaba da tallafawa jami’an tsaro da sahihan bayanan bata gari.
You must be logged in to post a comment Login