Labarai
Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun sako ƴan Kasuwar Kwari sama da 20 da aka sace
Ƴan bindiga sun sako ƴan kasuwar Kwari sama da 20 da suka sace a hanyar zuwa kasuwar Aba ta jihar Abia.
Jami’in yaɗa labaran kasuwar Alhaji Mansur Haruna Ɗandago ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio.
Ƴan kasuwar sun kwashe kwanaki biyar a hannun ƴan bindigar kafin a yanzu da suka sako su.
Alhaji Mansur ya ce, an sako su ne bayan da aka biya kuɗin fansa sai dai bai bayyana adadin kuɗin da aka biya ba.
Yanzu haka dai tuni ana saran isowarsu Kano kamar yadda ya shaida mana.
Ku kasance da labaran An Tashi Lafiya da ƙarfe 6 na safe domin jin cikakken labarin.
You must be logged in to post a comment Login