Connect with us

Labarai

Yanzu-yanzu : Buhari ya nada sabuwar shugabar hukumar NDDC

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Barista Joy Nunieh a matsayin shugaban hukumar kula da yankin Niger Delta.

Muhammadu Buhari ya dauke matakin ne bayan da ya sauke tsohon shugaban Farfesa Kemebradikumo Pondei, daga shugabancin hukumar sakamakon zargin sa da almundahanar kudade.

Shuagaba Buhari ya kuma kara adadin mutanen da ke cikin kwamitin binciken hukumar daga mutane uku zuwa biyar da.

Daga cikin wadanda aka nada akwai, daraktan tsare tsare na hukumar Cairo Ojougboh, da Mr. Ibanga Bassey Etang, mai rikon mukamin sashin kudi da mulki da kuma Mrs. Caroline Nagbo a matsayin mamba sai kuma  Cecilia Bukola Akintomide, OON, wadda tsohuwar shugaban bankin ci gaban afrika ce ita ma a matsayin mamba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!