Connect with us

Labarai

Da dumi-dumi : Za’a bude makarantun boko a watan Agusta

Published

on

Ma’aikatar ilimi ta kasa ta bayyana cewar za’a bude makarantu Boko a ranar 4 ga wata mai kamawa na Agusta.

Ma’aikatar ilimi ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter bayan kammala ganawa da kwamshinoni ilimi na jihohi 36 na kasar nan da babban birnin tarayya Abuja da kungiyar shugabanin masu makarantu ta kasa ta kafar Internet.

A cewar sanarwar wadanda za su rubuta jarrabawar kammala sakandire ne kadai za su koma makarantar.

Ana kuma sa ran cewar, daliban za su fara rubuta jarrabawa a ranar 17 ga watan Agustan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!