Labarai
Yanzu-yanzu: Kotu ta dakatar da shugabannin PDP ɓangaren Sagagi a Kano
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Kano ta dakatar da shugabancin jam’iyar PDP ƙarƙashin Shehu Sagagi.
Kotun ta dakatar da su tare da cewa ba za su ci gaba da shugabanci ba har sai ta gama sauraron ƙarar da a ka shigar a gaban ta.
Ana dai zargin Sagagi da biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyar NNPP na ƙasa Rabi’u Musa Kwankwaso.
Tun da fari dai wani mutum mai suna Bello Bichi ne ya shigar da ƙarar a gaban Mai Shari’a A. M. Bichi Yana ƙalubalantar PDP da INEC da sauran wasu mutane 40.
Kotun ta ce ta bada umarnin ne domin gujewa wani yanayi da za a zama babu shugabanci a jam’iyar, shi ya sanya ta bada umarnin ga wanda a ke ƙara na 3 har zuwa na 42 kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.
You must be logged in to post a comment Login